Tura

Kayan aiki

  1. Fulawa cup 2
  2. Sugar cokali 3 in kanaso yayi Zaki kasa biyar
  3. Yeast cokali 1
  4. Madara cup 1
  5. 1/4Gishiri
  6. Falevo kadan
  7. Ruwan dumi cup 1
  8. 1Kwai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Sa ruwa akan wuta kasa madara a ciki yayi dumi sai kasa yeast naka a cikin ruwan madara kasa kwai sai ka ajiye a jefe

  2. 2

    Kasa fulawa a kwano Mai kyau kasa sugar ka hadan su ka sa gishiri sai ka dauko ruwan madaran Nan ka zuba a ciki kayi ta bugawa har sai ya bugu sosai sai ka ajiye a waje Mai dumi ya tashi

  3. 3

    Ka sake dauko wa ka buga shi sai kayi Nadi twisting kenan ka sake ajiyewa ya tashi saika soya a cikin man gyada Mai zafi shikenan

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Fatima abba
Fatima abba @ummee2526
rannar

sharhai

Ummu_Zara
Ummu_Zara @ummu_zaraskitchen
Yayi kyau, ya ake nadin twisting?

Similar Recipes