Majestic yam

Abunda yasa nayi wannan hadi sabida ana gajiya da soyayyar doya, ko dafaffiya ko paten doya.. Shi yasa nayi tunanin inzo da wani samfari na musamman
Majestic yam
Abunda yasa nayi wannan hadi sabida ana gajiya da soyayyar doya, ko dafaffiya ko paten doya.. Shi yasa nayi tunanin inzo da wani samfari na musamman
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki fere doya sai ki yayyanka ta kamar gidan siga sai a tafasa Sama Sama tare da curry da Maggi.. In ta tafasa sai ki tsane ruwan sai kuma ki soya doyar cikin mai.. In ta soyu sai ki kwashe.. Daga nan zaki gyara karas dinki ki yanka dogaye dogaye, Shima Green pepper da tattasai duk dogaye zaki yanka ki wanke ki ajiye
- 2
Sai ki samu wata tukunya daban ki zuba mai kadan sai ku zuba grated onion ki soya.. Sai ki dauko jajjagaggen tarugu ki zuba ki zuba Maggi, gishiri da kayan kamshi... Sai ki zuba wannan yankakken karas da soyayyar doya a tare ki rufe ki barshi tsawon mintuna. Sai ki bude ki zuba tattasai da kika yanka da green pepper ki Motsa ki sauke... Shi kenan sai ki zuba kiyi garnishing da cucumber 😋😋
Similar Recipes
More Recipes



sharhai