Cup Cake
Zaki iya tarbon baki ko ayiwa oga ko Yara Don zuwa makaranta
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki fara daka sugar sai ki juye a bowl ki zuba butter ki ta juyawa in kina mixer kiyi amfani da ita in babu kiyi da whisker ko muciya. Zakiyi ta juyawa har sai sun hde jikin su Zaki ga yayi laushi sosai yai haske
- 2
Saki fasa kwai ki zuba ki kwada shi ya hde dasu butter din. Sai ki zuba flavor ki kawo fulawa da baking powder ki rinka zubawa a hankali kina juyawa har sai yayi daidai sai ki shafa butter a cups ki zuba hdin half ki gasa a oven.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/10646227




sharhai