Tuwon shinkafa miyan wake
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki gyara shinkafar ki tsaf ki wanke ta tas sannan ki zuba a tukunya kisa mata ruwa daedae yarda kike ga zai dafa maki shinkafae
- 2
Sae ki daura a saman wuta kisa wutan kadan domin ya dahu sosae
- 3
Bayan kin daura tuwon ki sae kizo ki surfa waken ki ki wanke shi sosae
- 4
Sannan ki jajjaga kayan miyan ki tarugu,tattasae,albasa
- 5
Sae ki zuba waken ki a tukunya ki zuba kayan miyan ki da manja,maggi,spices,da duk dukkan sauran sinadaran girki da sazu kara maki dan dani
- 6
Sae ki daura a saman wuta shima karki cika me wuta kamar tuwon ki,
- 7
Bayan shinkafar tuwon ta dahu kuma ta tsotse sae ki tuka ki kwashe a leda kisa a cooler
- 8
Sannan idan waken ki ya dahu sosae kuma komae na kayan dandano yaji,sae ki Dan faffasa waken koda muciya ko da ludayi domin miyan tayi laushi
Keywords
Similar Recipes
More Recipes




sharhai