Tuwon shinkafa miyan gyara da alayyahu

Tuwon shinkafa miyan gyara da alayyahu
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki gyara shinkafar tuwon ki tsaf ki wanke ki sa a tukunya ki zuba ruwa yarda zai dafa maki shinkafar sae ki daura a tukunya ki sa wuta kadan domin ya dahu sosae
- 2
Sannan ki gyara kayan miyan ki tarugu, tattasae, albasa ki markada ki zuba a tukunya ki daura a wuta ki zuba gishiri,spices sae ki bar Jan maggi sae daga baya sai ki barshi ya tsotse
- 3
Sannan ki gyara alayyahun ki ki yanka ki wanke da gishiri ki tsane a kwando
- 4
Sannan ki gyara gyadan ki shima ki dakata sama sama kar tayi laushi
- 5
Idan ruwan miyan ya tsotse sae ki zuba man gyada da sauran maggin da baki sa ba ki soya idan ta fara soyuwa sae ki zuba gyadan ki da kika gyara bayan nan sae ki barshi kmr minti 20 sannan sae ki zuba alayyahun ki da kika gyara ki rufe ki barshi tsawon mintuna 25 ko 20 sae ki sauke
- 6
Bayan tuwon ki ya tsane sai ki tuka ki kwashe a Leda kisa a cooler
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai