Awara 2
Foodfoliochallenge wannan awarar tanada dadi abaki gamu daukan ido
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki samu tuwan awaranki ki yanka da fadi,sai ki saka cookies cutter ki dinga dannawa kina debewa
- 2
Sai kisa gishiri da ajino moto da dan ruwa kadan ya game sai kisa awararki ki juya,sai kisa cikin mai mai zafi ki soya
- 3
Hadin sauce :zaki jajjaga/ markada/goga tattasai,tarugu,albasa tafarnuwa,danyar citta,kisa mai a wuta,kisa albasa da kika yanka,sai kisa hadin su tarugun kina juyawa,sai kisa maggi da kayan kamshi,ki juya,sai kisa albasa da kika yanka
- 4
Sai ki fasa kwai akai,kibashi second biyu sai ki dagargazashi har ya game jikinsa
- 5
Sai ki yanka kabeji siriri,ki wanke kintsane,sai ki wanke karas ki goga,ki yanka albasa sai ki jera
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11773699













sharhai