Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki hada busasun kayanki a guri daya bayan jin tankade fulawa sai ki murzasu ki mutsitsika su game jikinsu sai ki zuba ki kwaba kwabin kaman na meatpie kada yayi ruwa kada yayi tauri.
- 2
Ki kwaba ya hade jikinsa sai ki aje a gefe ki rufe ya tsimu sannan ki dako injin Murza taliya ki gutsuro kwabin fulawar ki dan fadada shi ki shafe da garin fulawa sai ki murza shi yanda kike da bukatarsa.Idan an gama wasu suna shan yawa ta bushe wasu kuma haka suke dafawa a danya,tana dadi a jallof,da miya ko Mai da Yaji.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/12805870




sharhai