Alale da sauce din hanta

Me gidana na matuqar son alale musamman a hadashi da sauce din hanta Yana qara lafia sosai
Alale da sauce din hanta
Me gidana na matuqar son alale musamman a hadashi da sauce din hanta Yana qara lafia sosai
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko xa a jiqa wake yayi kamar minti biyar ko goma,se a tsanyeshi a juye a turmi a sirfashi,idan yayi se a juye a roba me fadi a wankeshi sosai harse bawan waken ya fita
- 2
Se a jiqa waken da ruwa yayi kamar 10 minutes se a tsaneshi a juye a roba a wanke tarugu da tattasai da albasa a xuba a waken se akai engine a nuqa yayi laushi
- 3
Idan andawo daga niqa se a xuba ruwan xafi daidai misali yanda baxeyi ruwaba se a xuba mangyada daidai misali a daka cray fish a xuba a ciki da sinadarin dandano a juya sosai se asama Santana a qulla aciki
- 4
Se a daura ruwa ba dayawaba a tukunya idan ya tafasa a xuba alalen yayi kamar 45 minutes to 1 hour idan yabar ledan alamar yayi kenan se a sauke.
- 5
Se a jajjaga kayan Miya asa Mai a tukunya idan yayi xafi a xuba kayan miyan sannan asaka hantan aciki axuba curry da thyme da sinadarin dandano axuba garin citta aciki a rufe idan yayi a sauke...aci Dadi lafia
Similar Recipes
More Recipes



sharhai