Fish ball salad

Shi wannan salad zaka iya cinsa a matsayin abincin dare (dinner). Bashi da nauyi kuma ga saukin yi
Fish ball salad
Shi wannan salad zaka iya cinsa a matsayin abincin dare (dinner). Bashi da nauyi kuma ga saukin yi
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko za'a Fara hada wannan fish ball din, asamu tsokar kifi mara kaya sai a Samata kayan kamshi da kayan dandano, asaka jajjagagen attaruhu da albasa a juya su jade jikansu sai mulmula kamar kwallo a ajiye a fefe, sai a fasa kwai a dora mai a wuta yayi zafi sai a dinga tsoma mulmulallen kifin a cikin ruwan kwai ana tsamewa sai a birshineshi a cikin garin buredi sai a soya.
- 2
Yadda ake hada salad, za'a yanka ganyen lettuce, ayanka koren tattasai, tumatir da albasa. A Ajiyesu a gefe.
- 3
Asamu mai a zuba masa kayan Dan dano da kayan kamshi sai a ajiye a fefe.
- 4
A samu mazubi mai kyau a zuba ganyen lettuce din da aka yanka sai a zuba tumatir and albasa, a zuba Koren tattasai sai a yaryada wannan hadin mai da aka hada (salad dressing) sai a dauko wannan fish ball din da akayi a saka a gefe. Ayanka tumatir rose shape ayi ado dashi.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes




sharhai