Danbum shinkafa Recipe By RuNas kitchen

RuNas Kitchen @ChefR6044
Inason danbum shinkafa sosai #GARGAJIYA
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki tankade shinkafanki da aka barzo saiki wanke ki kawo gyada kizuba kijuya saiki dan tsaneta a kwando bawai ruwan ya tsane duka ba saiki turarata a steamer koh duk abinda kike turarawa dashi za tai yan mintina
- 2
To idan tayi saiki juye ta a mazubi dan babba saiki kawo albasa da attaruhu da tafarnuwanki daman kin yanka albasar Attaruhu kin jajjaga da tafarnuwa saiki zuba da mai kijuya komai ya hade
- 3
Saiki kawo maggi da curry kizuba shima kijuya saiki maida kan wuta cikin steamer dinki ya karasa turarowa idan yayi zakiji kanshi yana tashi
- 4
Zaki iya saka kifi aci dashi
- 5
✍🏻Written by
*Rukayya m jamil*
*Mrs Nasir *
CEO
👩🍳RuNas Kitchen👩🍳
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16026752










sharhai