Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaa gyara rama a yanka kanana a wanke a tsameshi a ajiye a rife.
- 2
A gyara kayan miya tsab a markada ko jajjaga a zuba a tukunya.
- 3
A daka gyada a ajoyeshi.
- 4
Sannan sai a tafasa idan da hali in kuma babu zaa iya sa wake.
- 5
Bayan nan sai a dora kayan miya asa manja a dan soya saan nan a kawo kayan kamshi da na miya azuba a da ruwa daidai sanwa a rufe.
- 6
Daga bisani in ya tafasa sai a zuba rama,a zuba gyadan a rude har ya hadu yayi kauri.
- 7
Idan tsamin ya danyi yawa sai a dan sa kanwa don rage tsamin.
- 8
Zaa iya ci da ko wani irin tuwo.
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16495128



sharhai (2)