Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki jika wake ki surfe,sai ki wanke zaki ga dussan waken asama shi zaki zubar idan waken ya wanku sai ki rege koda kasa aciki
- 2
Sai ki gyara tarugu,tattatsai,albasa da tafarnuwa ki wanke kisa acikin waken,zaki nika da laushi idan kin nika sai kisa magi da manja amma kar kisa manjan duka zaki rage Wanda zaki sa a gwan gwani
- 3
Sai ki kara ruwa kisa kayan kamshi amma kar yayi kauri kuma kar yayi ruwa idan kin gama juyawa,zaki dafa kwai ki bare bayan sai ki yanka kanana ki zuba acikin kullin sai kisa manja a gwan gwani ko ina ya samu ki zuba kullin aciki,zaki samu tukunya kisa murfin samaira aciki kisa ruwa kar ya hau saman sai ki jera alalan aciki ki rufe da kyau sai ki barahi ya nuna aci lafiya
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/7935949





sharhai (4)