Dublan

Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
Kaduna

Yanayin yadda aka kawata dublan din kadai ya isa ya jawo hankalin duk wanda aka ajje a gabanshi. Kar koyaushe ayita yin irin abin da kowa yake yi. Ki yi kokari ki kirkiri naki salon domin ki burge duk wa'yanda suke zagaye da ke.

Dublan

Yanayin yadda aka kawata dublan din kadai ya isa ya jawo hankalin duk wanda aka ajje a gabanshi. Kar koyaushe ayita yin irin abin da kowa yake yi. Ki yi kokari ki kirkiri naki salon domin ki burge duk wa'yanda suke zagaye da ke.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Filawa kofi biyu
  2. Bota cokali daya
  3. Gishiri tsakuren yatsu
  4. Bekin hoda rabin cokalin shayi
  5. Mai saboda soyawa
  6. Bayan kin gama za ki bukaci
  7. Narkakken suga mai lemun tsami
  8. Sprinkles
  9. Da kuma robo (smaties)

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ga abubuwan bukata a nan

  2. 2

    Ki zuba bota a cikin roba mai dan fadi. Sai ki zuba gishiri da bekin hoda

  3. 3

    Sai ki motse su sosai

  4. 4

    Ki zuba filawa da kuMa ruwa ba mai yawa ba

  5. 5

    Sai ki murza sosai. Idan da Bukatar karin ruwa sai ki kara kadan ba mai yawa ba

  6. 6

    Ki zuba filawa a abun murzawa ki baje ko'ina da shi. Ki dora filawar a kai ki buga sosai

  7. 7

    Sai ki rarraba shi, ki yi kokari girman ya daidaita. Na raba shi kashi biyar

  8. 8

    Sai ki baza shi a abun murzawa ya yi fadi. Ki daidaita shi kamar yadda na yi

  9. 9

    Sai ki bar guda daya ki dauke guda daya. Ki ninka wanda kika bari din kamar haka

  10. 10

    Ki yi amfani da wuka ko kuma abun yanka Pizza. Ki yanka shi sirara kaman haka

  11. 11

    Sai ki bude shi

  12. 12

    Ki bi karshe da karshen ki shafa damammiyar filawa don ya like sosai ko ya shiga mai ba zai warware ba. Ki dauko gefe guda ki dora kan guda

  13. 13

    Ki dauko gefe da gefen ma ki cusa a ciki sai ki like shi da yatsunki

  14. 14

    Kin ga yadda za su zama nan

  15. 15

    Sai ki zuba mai a kasko ki dora a wuta. Idan ya yi zafi ki zuba dublan din a ciki

  16. 16

    Ki rinka yi kina motsawa a hankali. Kuma wuta Kadan za ki sakar masa

  17. 17

    Sai ki tsane a gwagwar Karfe idan ya soyu

  18. 18

    Ki zuba sugar kofi daya a tukunya da ruwan lemon tsami kofi daya. ki kunna wuta a hankali har sugan ya narke. ki barshi ya huce. Bayan ya huce sai ki rinka tsoma dublan din a ciki ya jima sannan ki fitar

  19. 19

    Bayan na gama duka na zuba sprinkle da robo a kai. Za ki iya amfani da ridi ko habbatussaudah ki saka shima yana dadi sosai

  20. 20

    Akwai dadi sosai

  21. 21

    ❤❤❤

  22. 22
  23. 23
Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
rannar
Kaduna
I absolutely love cooking. I can merrily state that my kitchen is my playground in every sense! My mother has always been a wonderful cook, and I feel she is my inspiration.
Kara karantawa

sharhai (11)

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
Kayan marmari masu dadi 😋 gashi kuma an zuba fasaha masha Allah

Similar Recipes