Kosai

Kosai nada matukan mahimmanci ajikin dan adam musamman anso a rinka na ma yara ,saboda wake kuma na hada da kwai ,wake nada mahimmanci saboda protein ne iyalaina nason kosai musamman inyi shi da kunun tamba #kosaicontest
Kosai
Kosai nada matukan mahimmanci ajikin dan adam musamman anso a rinka na ma yara ,saboda wake kuma na hada da kwai ,wake nada mahimmanci saboda protein ne iyalaina nason kosai musamman inyi shi da kunun tamba #kosaicontest
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko nasa wake a roba sai na zuba ruwa kofi biyu na bar waken ya jiku na minti biyu,da lokacin yayi sai na tsane ruwan nasa wake acikin turmi na surfa amma bana dakawa da karfi saboda kar waken ya farfashe sai ki kwashe kisa acikin roba
- 2
Sai kisa ruwa sosai saboda dussan ya taso sama kaman haka
- 3
Sai kisamu kolanda ki zuba ruwa waken ahankali zakiga dussan acikin colanda waken a roba sai ki kara sa ruwa ki tayin haka har waken ya zama ba hancin waken, sai ki tsince sauran dattin da hannu kisa ruwa acikin waken ki samu wani roba kina iban waken kina sawa acikin dayan roban har kizo karshe zakiga du watsu sai ki zubar
- 4
Gashi na wanke na gyara sai kisa ruwa Kofi daya acikin waken ki barshi yayi minti biyu, kafin lokacin yayi sai ki gyara albasa da tattasi ki wanke kisa acikin waken sai ki kai nika idan zaki kai kisa karamin roba aciki saboda kar acika ruwa
- 5
Gashi an nika sai nasa gishiri,magi da kwai,na samu ludayi na buga sosai har na minti biyar
- 6
Gashi na buga,sai nasa kaskon suya akan wuta nasa mangyada da yayi zafi sai na rinka iban kullin inasawa acikin mangyada
- 7
Gashi na gama sawa da yayi ja sai na juya shima da yayi sai na samu abin tsama ma kwashe zaki iya ci da kunu
- 8
Idan zakiyi yaji zakisa barkono a turmi kisa magi,citta da kanin fari sai ki daka yayi laushi kisa a roba
Similar Recipes
More Recipes


















sharhai