Miyar wake tuwon shinkafa

Masu dafa abinci 9 suna shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Wake kofi biyu
  2. Manja rabin kofi
  3. Nama kofi daya
  4. Kifi
  5. Maggi
  6. Gishiri
  7. Tumatir
  8. Attarugu
  9. Tattasai
  10. Albasa
  11. Lawashi
  12. Citta cokali daya karami
  13. Tafarnuwacokali daya karami
  14. Ruwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaa jika wake yayi minti biyar,sannan a surfa a wanke sosai a cire bawo da kasa

  2. 2

    Zaa zuba wake a tukunya, azuba ruwa kofi hudu a barshi ya dahu sosai

  3. 3

    Zaa jajjaga kayan miya da albasa, a zuba manja a tukunya a soya a saka naman da aka yanka kanana hade da kayan miya a soya sosai

  4. 4

    Idan kayan miya suka soyu sosai zaa.zuba ruwa kofi daya da rabi, asaka maggi, gishiri, citta da tafarnuwa, abarshi ya dahu na tsawon mintuna biyar, sannan asaka kifi (soyayye akayi anfani dashi), lawashin albasa da kuma dafaffen waken mu, ajuya sosai arufe tukunya, arage wuta sosai abarshi ya.dahu

  5. 5

    Idan aka bude tukunya aka ga mai ya taso to miyar tayi se a saukar.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Jantullu'sbakery
Jantullu'sbakery @jantulluhadiza84
rannar
Sokoto
I love cooking,i love been creative and I love sharing my recipies 💓❣️💃
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes