Dafadukan shinkafa da salad

Ummu Khausar Kitchen @1987kau
Ina son dafadukan shinkafa garaugarau shi yasa nake yawan yi
Dafadukan shinkafa da salad
Ina son dafadukan shinkafa garaugarau shi yasa nake yawan yi
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki gyara kayan miya ki jajjaga
- 2
Sai ki kunna wutar ki,ki daura tukunya ki zuba mai madaidaici
- 3
Saiki zuba kayan miya ki soya sama sama sai ki tsayar da ruwanki ki,sai ki kawo su Maggi da gishirin duk ki zuba ki barshi ya tafasa
- 4
Sai ki wanke shinkafa ki zuba,in ta kusa dahuwa sai ka kawo ounga da gino a zuba abarta ta nuna
- 5
Sai ki dauko salad dinki ki gyara ki wanke tas tare da tumatir da albasa sai ki zuba kan abincin bayan kin zuba a plate sai ki yaryada cream salad.
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/8760654



sharhai