Dambun doya

#Iftarrecipecontest,hanyoyin sarrafa doya dayawa,shiyasa na yanke shawarar yin dambunta a lokacin yin SAHUR.Yana da dadi sosai.
Dambun doya
#Iftarrecipecontest,hanyoyin sarrafa doya dayawa,shiyasa na yanke shawarar yin dambunta a lokacin yin SAHUR.Yana da dadi sosai.
Umarnin dafa abinci
- 1
Ga kayan hadin mu
- 2
Da farko za'a fere doyar a dafa,sannan a murmusa,sai a ajiye a gefe.Sannan a gyara kayan miyar,adan soya sama-sama da mangyada da maggi, sai azuba acikin doyar a jujjuya.. Kamar haka
- 3
Sai a kada kwai,a zuba,a jujjuya, adan kara maggi kadan
- 4
Sai a zuba cikin abin tuyar kwai(frying pan) a kuma bi da ruwan kawai da dan mangyada,sai ayi ta juyawa na minti goma.Sannan a sauke
- 5
Yadda za'a hada sos din dana hada da doyar.
- 6
Za'a jajjaga kayan miyar,Sannan a zuba mangyada a abin tuyar kwai(frying pan)..sai a zuba kayan miyar,a sanya maggi mai dandano da gyadar miya(nutmeg) Sannan a jujjuya na tsahon mintuna sha boyar,Sannan sauke a cakuda da doyar,kamar yadda nayi bayani a sama.
- 7
Ga sakamakon.Aci lafiya da shayi koda shinkafa.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

















sharhai (6)