Kunun alkama

Kunun alkama na da dadi sosai, ga kuma amfani a jikin domin yana taimakawa wajen digestion da kuma movement of bowel.
Kunun alkama
Kunun alkama na da dadi sosai, ga kuma amfani a jikin domin yana taimakawa wajen digestion da kuma movement of bowel.
Umarnin dafa abinci
- 1
Zuba alkama a turmi kisa ruwa kadan ki daka sama sama domin bayan ya fita ba tare da alkamar ta farfashe ba sannan se ki baza ta a rana ta sha iska
- 2
Idan ta sha iska zaki ga bayan ya rabu da jikin alkamar se ki fece (bakace) dusar, ku kula ba'a wanke alkama saboda tana da danko sosai, idan kin wanke zaki ga duk ta hade jikinta ba zata kyau ba
- 3
Zuba ruwa mai tsabta a tukunya ki dora a wuta ki barshi ya tafasa. Idan ruwan ya tafasa se ki zuba alkama da sikari da kuma gishiri katan ki barshi yayi ta dahuwa har se alkamar ta farfashe tayi laushi.
- 4
Sannan se ki kwaba Cornflour da madara, idan madarar ruwa kika yi amfani dashi, ba se kin sa ruwa a hadin ba.
- 5
Ki zuba wannan hadin na madara da cornflour a cikin alkamar da ke kan wuta kina ci gaba da juyawa har se kunun yayi kauri. Ki kula wannan kunu ana dafa shi tare da sugar don kar ya tsinke, idan kika ce se kin sauke zaki saka sikari to zaya tsinke duk yanda yayi kauri kuwa.
- 6
Idan yayi kaurin da kike so se ki sauke. Shikenan kunun alkama ya hadu.
Similar Recipes
More Recipes



sharhai