Fanke mai kala

Salwise's Kitchen @cook_16516066
#Iftarricipecontest,ina son naga hanyoyin sarrafa abinci daban-daban,shiyasa nayi wannan fanke mai kalar ja.
Fanke mai kala
#Iftarricipecontest,ina son naga hanyoyin sarrafa abinci daban-daban,shiyasa nayi wannan fanke mai kalar ja.
Umarnin dafa abinci
- 1
Ga kayan hadin mu, kamar haka
- 2
Da farko za'a jika yist da sikari da bakar hoda, cikin ruwan dumi na mintoci biyar,za'a ga ya kumburo kamar haka
- 3
Sai a dauko fulawar a zuba gishiri
- 4
Sai azuba madarar
- 5
Sannan a zuba yist,sikari da bakar hodar da aka jika a jujjuya
- 6
Sannan a zuba kalar ja
- 7
Sai a jujjuya, a rufe a barshi yayi mintoci talatin
- 8
Za'a ga ya kumburo kamar haka
- 9
Sai a sanya mangyada a wuta yayi zafi sannan a rika diba ana zubawa har agama,idan yàyi a kwashe.Sai ci
- 10
Ga sakamakon.Asha ruwa lafiya
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/8969133














sharhai