Farfesun naman karamar dabba

Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
Kano, Meduguri Road, Tarauni.

Wayyo anan gun ba a magana, Idan ina shan roman sa musamman ya dahu yayi luguf har naman ya fara fita daga kashin akwai dadi kana sha kana kurbar roman nama.....#1post1hope

Farfesun naman karamar dabba

Wayyo anan gun ba a magana, Idan ina shan roman sa musamman ya dahu yayi luguf har naman ya fara fita daga kashin akwai dadi kana sha kana kurbar roman nama.....#1post1hope

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Naman karamar dabba
  2. Jajjagen attaruhu da albasa Wanda aka tafasa
  3. Tafarnuwadomin bukata
  4. Mai kadan
  5. Lemon tsami
  6. Kayan dandano
  7. Kayan kamshi
  8. Curry
  9. Dakakkiyar citta wadda taji kayan hadin gargajiya
  10. Koren tattasai
  11. Yankakkiyar albasa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    A sami roba a juye naman sai a gyara shi a rage masa kitse Idan yankan manya ne a yayyanka ya dawo madaidaita. Sai a zuba ruwa a yanka lemon tsami a wanke sosai da Sosai.

  2. 2

    A juye a tukunya a Dora a wuta, sannan a zuba yankakkiyar albasa, curry, kayan dandano, kayan kamshi, citta sannan a daka tafarnuwa a zuba Idan ana bukata a zuba wadataccen ruwa a rufe yayi ta dahuwa.

  3. 3

    Idan ya dahu ruwan ya zama Rabi sai a zuba mai, attaruhu da albasa a Dan kara kayan kamshi Idan magi bejiba ba a kara sai sake rufewa.

  4. 4

    Mintuna 10 sai a kawo yankakken Koren tattasai da albasa a zuba akai a rufe sai a kashe wutar. Minti 5 da saukewa sai a kwashe. An fison sa da romon romo.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
rannar
Kano, Meduguri Road, Tarauni.
cooking is my dream!!!
Kara karantawa

Similar Recipes