Tura

Kayan aiki

awa daya
uku
  1. Fulawa kofi biyu
  2. Gishiri kadan
  3. Corn fulawa karamin chokali daya
  4. Mai
  5. Maggi daya
  6. Kori kadan
  7. Kabeji karami
  8. Karas guda hudu
  9. Albasa 1 maidan girma
  10. Jajjagaggen tarugu da tattasai chokali daya

Umarnin dafa abinci

awa daya
  1. 1

    Zaki hada fulawa da mai da da corn fulawa da gishiri saikisa ruwa ki kwaba, kamar kwabin samosa, ki aje yayi kamar minti talatin saiki dauko mi kara murzashi ki rabashi gida uku

  2. 2

    Zaki zuba mai a pan kisa gurzajjen karan idan yayi minti biyar saikisa kabeji da albasa ki juyasu sosai

  3. 3

    Saikisa maggi da kori da jajjagaggen tarugu da tattasai, saiki kara juyawa, komai ya hade jikinshi, idan yayi minti biyu saiki sauke

  4. 4

    Ki barbada fulawa ki murza kwabin fulawarki yayi fadi saiki kawo hadinki kisa a gefen, saiki nade, Ki kwaba fulawa da ruwa yayi kauri, saiki Shafa a karshen

  5. 5

    Saiki sa yuka ki yanke, saiki raba gida uku ko hudu, yadan ganta da tsawon shi

  6. 6

    Haka zakiyi sai fulawar ta kare, idan zaki soya saiki sa karshe karshen cikin fulawar da kika dama da ruwa

  7. 7

    Saiki dora mai a wuta idan yayi zafi saikisa ki soya, shikenan aci dadi lafiya...........

  8. 8
Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Umman Amir And Minaal 🎂🍜🍝
rannar
Nigeria
........ I like cooking very much.....and I like been in the kitchen all the time, I'm proud of my self 💟💟💟
Kara karantawa

Similar Recipes