Fanke mai kala

Salwise's Kitchen
Salwise's Kitchen @cook_16516066
Zaria

#Iftarricipecontest,ina son naga hanyoyin sarrafa abinci daban-daban,shiyasa nayi wannan fanke mai kalar ja.

Fanke mai kala

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

#Iftarricipecontest,ina son naga hanyoyin sarrafa abinci daban-daban,shiyasa nayi wannan fanke mai kalar ja.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Minti arba'in
Mutane biyar
  1. Fulawa gwangwani biyu
  2. Sikari cokali biyar
  3. Yist cokali daya karami
  4. cokaliBakar hoda rabin karamin
  5. Madarar gari babban cokali daya
  6. Gishiri dan kadan
  7. Ruwan dumi
  8. Kala ja murfi biyu

Umarnin dafa abinci

Minti arba'in
  1. 1

    Ga kayan hadin mu, kamar haka

  2. 2

    Da farko za'a jika yist da sikari da bakar hoda, cikin ruwan dumi na mintoci biyar,za'a ga ya kumburo kamar haka

  3. 3

    Sai a dauko fulawar a zuba gishiri

  4. 4

    Sai azuba madarar

  5. 5

    Sannan a zuba yist,sikari da bakar hodar da aka jika a jujjuya

  6. 6

    Sannan a zuba kalar ja

  7. 7

    Sai a jujjuya, a rufe a barshi yayi mintoci talatin

  8. 8

    Za'a ga ya kumburo kamar haka

  9. 9

    Sai a sanya mangyada a wuta yayi zafi sannan a rika diba ana zubawa har agama,idan yàyi a kwashe.Sai ci

  10. 10

    Ga sakamakon.Asha ruwa lafiya

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Salwise's Kitchen
Salwise's Kitchen @cook_16516066
rannar
Zaria
I was born and bred up in Zaria
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes