Kwallon dankalin Hausa

Idan kina/kana son kwallon dankalin turawa, to Zaki so kwallon dankalin hausa. A gwada ma Yara da maigida.
#kadunastate
Kwallon dankalin Hausa
Idan kina/kana son kwallon dankalin turawa, to Zaki so kwallon dankalin hausa. A gwada ma Yara da maigida.
#kadunastate
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko, Zaki fere dankalin hausan ki, sai ki yayyanka su, ki wanke, ki sa a cikin tukunya, ki zuba ruwa, sai ki sa gishiri, ki daura akan wuta.
- 2
Idan dankalin ki ya nuna, sai ki sa a karamin turmi, ki daka shi har sai ya yi laushi.
- 3
Sai ki juye dakakken dankalin a roba ko kwano, sai ki sa sinadarin dandano, ba sai an sa gishiri ba saboda an sa a dahuwan dankalin, (Amma in ana da bukatan karawa, ana iya sa gishiri kadan).
- 4
Sai ki jajjaga tarugu da albasa, ki zuba a cikin dankalin, ki tafasa kifin ki da gishiri da albasa, sai ki zuba a cikin dankalin.
- 5
Ki juya da kyau, ki tabbatar komi ya hade, sai ki dinga diba ki na mulmula su zuwa kwallaye.
- 6
Sai ki dauki kowane kwallo, ki tsoma a cikin kwai, sai ki tsoma a cikin barbaden burodi. Sai ki sa Mai a wuta, ki yanka albasa a Kai, idan ya yi zapi, sai ki jera kwallon dankalin ki a cikin man, har sai ya soyu. Sai ki kwashe. Shikenan kwallon dankalin Hausa ya hadu.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai