Danbum shinkafa
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki debi shinkafarki sae ki kai abarza miki kamar haka
- 2
Sae ki sheka mata ruwa ruwa kamar ynda Kika San anawa garin kwaki jiko,kina zuvawa sae ki tsiyaye
- 3
Bayan kin tsiyaye zata sae ki saka tsaftataccen hannunki sae ki motsashi har Wanda be samu ruwa ba duk sae ku hade
- 4
Sae ki rufeshi ki barshi kincigaba da aikinki,ki samo zogale yawan ynd kikeso ta fito sae ki tsigeta ki yanka da wuka,sae ki wanketa,ki saka cikin gwagwa
- 5
Sae ki wanke tarugu da tattasae inki ki saka cikin abin barzo wato hand blender ko kuma cikin blender sae ki wanke albasa 2 kinyankata cikin abin barxonki sae ki barzasu
- 6
Sae ki wanke karas inki ki yayyankashi duk yanda kikeson shape inshi y hito,sae sauran Albasa guda biyu ki yankata yankan zobe(Circle) kenan sae ki daurayesu ki saka cikin gwagwa kamar haka
- 7
Ynx sae ki koma gurin shinkafarki da kika rufe ki motsata, Zaki sameta har ta Dan fara taushi
- 8
Sae ki kawo zogalenki ki zuba sae ki motse da tsaftataccen hannunki
- 9
Sae ki kawo Farin magginki,Gishiri,Curry,Dakakken maggi,garin lawashi,garin gurfa sae ki zuba akai sae ki motse
- 10
Sae ki kawo barzazzun kayan miyanki ki zuba,awannan matakin kina iya saka babban cokali gurin motsawar sbd yajinda tarugu da tattasae suke dashi
- 11
Hadinki y kammala sae ki daura tsaftataccen madambacinki kan murhu,ki tabbatar ruwanda Kika saka qasa bazasu tabo danbunki ba,sae ki kawo hadin dambunki ki zuba,kiyi Mai rame tsakiya saboda fitar suraci sae ki rufeshi ruf
- 12
Idan dambunki yayi minti ashirin da biyar da daurawa sae kixo ki budeshi ki tattadashi ki zubamai Karas da Albasa,sae ki debi ruwa kamar rabin kofi haka ki yayyafa mai sae ki sake tonashi,ki rufe ruf
- 13
Sae ki soya Mai ki kadamai albasa ciki
- 14
Bayan minti 20 kamshin dambun ki y gama mamaye ko ina kuma koda Zaki dubashi insha Allah yayi taushi sosae😊
- 15
Sae ki samu babban roba ki zubashi ciki ki zuba Mai ki hadesu,dambu y kammala sae ciiii😋
- 16
JAN HANKaLI:-Irin wannan cokalinne nike magana(cokali ne na roba,irin na Wanda ake amfani dashi ma take away innan?
Keywords
Similar Recipes
More Recipes




















sharhai (5)