Funkaso da miyar taushe

Funkaso da miyar taushe
Steps
- 1
Da farko zaki samu garin alkamar ki saiki tankade ki zuba cikin bowl saiki tankade fulawa kiyi mixing dinsu saiki zuba gishiri kadan da maggi suma ki jujjuya then ki zuba yeast dinki da baking powder ki kara mixing saikiyi grating din attaruhu da albasan ki ki juye aciki ki kara jujjuyawa saiki zuba ruwa kadan ki saka muciya ki jujjuya da kauri ake kwabin inkin gama saiki rufe ki saka a cikin rana ko guri mai dumi.
- 2
Zaki wanke kayan miyanki bamai yawa ba kiyi Blanding dinshi saiki daura tukunyar ki, ki zuba mai in yayi zafi ki zuba kayan miyan har zuwa time din dazai tafaso ki zuba baking powder saiki wanke namanki ki saka aciki ki yayyanka albasa da yawa ki zuba ki daka gyadar ki itama ki zuba saiki bare kabewa itama ki juye saiki zuba ruwa ki saka murfi ki rufe.
- 3
Har zuwa time din da zakiga kabewarki ta dahu saiki ciccireta aciki ki saka cikin wani kwanon ki saka ludayinki ki damata saiki mayar cikin miyar ki zuba maggi da gishiri saiki rufe, ki wanke alayyahunki saiki yayyanka ki kara wankewa ki zuba a quallender har zuwa time din da zaki tabbatar gyadarki ta dahu saiki duba in kina bukatar karin maggi ki kara saiki juye alayyahun ki, ki saka curry ki jujjuya saiki rufe tsahon 3 minutes miyar taushenki tayi.
- 4
Saiki duba kwabin funkason ki inya tashi saiki zuba mai acikin kasko in yayi zafi saiki dauko wani karamin plate kina shafa mai acikinsa kina dauko kullin funkason ki kina daurawa akai ki faffada saiki saka dan yatsanki kina bude tsakiyar kina sawa cikin mai a haka harki gama.
Similar Recipes
More Recipes
-

Arezu
-

Prithika
-

Mallika Ramshatriya
-

Hiroko Liston
-

Hiroko Liston
-

Crock Pot Girl 🤡
-

Sarvat Hanif
-

Cauliflower "Mac" and Cheese (Keto friendly)
StephieCanCook
-

Sotay
-

Chef Weird Beard
-

Sotay
-

Mashed Cauliflower (87 calories)
Bill Landwehr -

Umma Sisinmama
-

nance -

Ifeanyichukwu Newsong Cajetan
-

🌈NinjaMommaKitchen🌈
-

Ifeanyichukwu Newsong Cajetan
-

Resham Naheed
-

Ifeanyichukwu Newsong Cajetan
-

lindschap













Comments