Soyayyar doya da farfesun kafar sa
Uhmmmm dadin ba'a mgn 😋😋😋
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko Zaki fere doya sai ki yanka ki daura ruwa a wuta in ya tafasa ki wanke doyar ki zuba da Dan gishiri. Tafasa biyu ta Isa sai ki tsane a colander ki daura Mai a wuta yai zafi sai ki soya doyar.
- 2
Zaki samu kafar sa da aka Riga a babbake aka wanke ta. Sai ki jajjaga su attaruhun ki daura tukunya a wuta ki zuba Mai ki soya jajjagen sama2 sai ki tsaida ruwa in ya tafaso ki kawo su kayan kamshi da dandano da garlic powder ki zuba da kafar sa din ki barta Tai ta dahu har sai ta dahu luguf. Za'a iya ci da soyayyen dankali ko doya.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/10321062




sharhai