Tuwon shinkafa miyar kubewa bushashshiya
Umarnin dafa abinci
- 1
A tsince shinkafar tuwo sosai sai a daura ruwa a wuta dai dai yadda zai dafa tuwon basai ana karawa ba. In ya tafasa a wanke shinkafar a zuba a juya da muciya kar ta dankare adan saba murfin ya dahu in ruwan ya tsotse sai a tuka abarshi ya turara sai a kwashe a zuba a cooler.
- 2
A soya manja da albasa sannan a tsaida ruwan miya akawo wake a zuba bayan an dauraye asaka banda kifi da daddawa da attaruhu da albasa a rufe ya tafaso asaka kanwa kadan waken ya dahu sannan a zuba dandano ya dahu a kada.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/8984714





sharhai