Sinasir da perpesun kayan ciki

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Sinasir abincine na alfarma da daraja awajajenmu na borno sbd anasonshi sosai#1post1hope

Sinasir da perpesun kayan ciki

Masu dafa abinci 5 suna shirin yin wannan

Sinasir abincine na alfarma da daraja awajajenmu na borno sbd anasonshi sosai#1post1hope

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafar tuwo kofi biyar
  2. Wake kofi daya
  3. Yeast chokali biyu
  4. Bakar foda chokali daya
  5. Suga chokali uku
  6. Gishiri rabin chikali
  7. Fulawa kofi daya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko nagyara shinkafata nawanketa dakyau nacire dukkan dattin dake ciki sai nadiba kofi daya aciki nazuba a tukunya nasa ruwa nadaura a wuta. Sai najika sauran kuma. Bayan najika sai nawanke wakena nacire dutsar tas. Shima najikashi. Bayan nakan wutan yanuna sosai sai najuye a tire don yahuce. Bayan yahuce sai nahadasu da wanda najikan da waken nacakudasu.

  2. 2

    Sai nazuba a roba mai tsapta nakai aka markadamin ita sai Nazi nazuba yeast da bakar foda da suga da gishiri na jujjuya sai natankade fulawa nazuba nasake jujjuyawa da kyau sai narufe na ajiye awuri mai dumi don yatashi

  3. 3

    Bayan yatashi sai nadaura pan awuta(pan wanda baya kamawa) sai nabarshi yayi zafi sai nazuba mai chokali daya bayan nazuba sai nadiba kullin nazuba narage wuta sai nadau murfin tukunya narufeta nabarta zuwa minti biyar ko bakwai haka sai nabude nagani. Sai naga yayi kyau gashi yayi idanu mai kyau kuma yanuna sai nacire nasake zuba wani.

  4. 4

    Wanda naciren sai nashafamata mai kadan a kai sai nasake cire dayan shikuma sai nakifeta akan dayar sai nasake shafa mai a bayan haka naringayi har nagama

  5. 5

    Note... Abunda yasa nasa wake aciki saboda zai karawa sinasir din kyau dakuma dadi kuma zai saka idanu manya manya sosai don haka mamata takoyamin. Mai kuma danake shafawa akai bayan nacire shikuma zaisa sinasir din yakara laushi sosai

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes