Tura

Kayan aiki

  1. Kifi
  2. Tafarnuwa
  3. Albasa
  4. Attarugu
  5. Citta
  6. Cinnamon
  7. Supreme spice
  8. Dankalin turawa
  9. Cabbage
  10. Lemon tsami
  11. Maggi Doli red
  12. Veg.oil

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko na wanke kifi, na barshi ya tsane ruwa na tsawon mintuna Ashirin

  2. 2

    Na daka tafarnuwa da citta, na saka a roba na zuba mangyada cokali abinci 3, na zuba maggi red,cinnamon, supreme spice na juya sosai

  3. 3

    Na dauko kifi na yi mishi yanka yanka ajikin sa kafin na fara dura masha wannan hadin man da nayi dana gama durawa acikin yanka yanka da nayi da cikin kai da cikin cikin kifi, sena shafa masa ajiki duka na barshi ajiye acikin friedge na tsawon Awa daya

  4. 4

    Na yanka lemon tsami na dora asama da kasan kifin(amfani idan kifin yana gasuwa wannan kamshin lemon yana ratsawa acikin kifin)na saka a oven na gasa na tsawon mintuna talatin

  5. 5

    A yayin da kifi ke gasuwa na fere dankali na wanke na yanke na soya, na kuna yanka cabbage, na kuma hada source na Albasa, attarugu, tafarnuwa, maggi red da mangyada kadan

  6. 6

    Da kifin ya gasu na dora na plate na zuba cabbage, dankali da source, nayi garnishing da lemon tsami(ina jin dadin kifi da lemon tsami, ina ci ina matsa ruwan lemon akwai dadi gsky)

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Jantullu'sbakery
Jantullu'sbakery @jantulluhadiza84
rannar
Sokoto
I love cooking,i love been creative and I love sharing my recipies 💓❣️💃
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes