Hanjin ligidi mai yoghurt

R@shows Cuisine
R@shows Cuisine @rashows_5946
Samaru Zaria,Kaduna

Hanjin ligidi,alawa CE da aka dade anayi tun zàmanin kakanninmu,yanzu kuma gashi nakara masa armashi,mun Kara zamanartar dashi tahanya Kara yoghurt, sbd yayi gardi.Asha dadi lfy.Nasadaukar GA @Ayshat_maduwa65 @Jamitunau @cookingwithseki @4321ss

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

  1. 2 cupsSugar
  2. Yoghurt gora daya ko rabi
  3. Ruwa Kofi daya
  4. Kwararo nazubawa
  5. Kwano cike da dussa
  6. Straw ki yanka kanana dai dai rikewa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko zaki tanadi kayan hadi kamar haka

  2. 2

    Sai kizuba sukari acikin tukunya kisa ruwa, ki Dora kan wuta,kibarshi yayi ta nuna,sai kinga yadauko nuna,sai kizuba yoghurt dinki,kiyi ta juyawa har sai kinga ya koma kalar brown,maana sugar tayi duhu.Amma karki bartata kone,zaki iya debowa da cokali,kisa yatsarki a ruwa ki dangwalo,dakin ganshi yana danko sosai yanuna.

  3. 3

    Sai ki dauko kwaroronki,ki sossoka a kwanonki me dussa,sai ki dinga dibo sugar nan kina sawa,bayan kingama zubawa,ki dauko straw ki SA ko tsinken kwakwa,tazama abin rikewa.kibarshi ya huce.Asha zaki lfy.

  4. 4

    KARIN BAYANI.
    In zaki zuba anaso kirinka sawa da sauri, sbd saurin huce wa,yakeyi zai daskare a tukunya.SANNAN ko biyoni a TIPS,zan nuna maku yadda ake Nada kwararo.ngd.pls inkin gwada kimin cooksnap. Kuma inzakiyi shi a Sanaa,zaki ji dadi sbd harmanya sha suke sbd yoghurt din dake ciki,akwai gardi sosai

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan

sharhai (7)

Fatima Ummi Tunau
Fatima Ummi Tunau @ummitee
Will sure try this one day in sha Allah

Wanda aka rubuta daga

R@shows Cuisine
R@shows Cuisine @rashows_5946
rannar
Samaru Zaria,Kaduna

Similar Recipes

More Recommended Recipes