Cake mai tabin strawberry

Wannan cake asali wajen Maryama's kitchen na ganshi ta yi cupcake da recipe din.
Na yi qare-qare a nawa, kamar na kala da cream....amma dai gaba daya yabawar tata ce.
Na yi girkin ne tun watan agustan 2020,dalilin kwadayi irin na lokacinnan na wata😁cikin dare har na kwanta na tashi na yi,ban samu damar daurawa ba sai yanzu.....
Babbar sadaukarwa ga Bint's Cuisine💕 Da Maman Jafar🤗💕na gode muku na kuma yi kewarku da cookpad duka.
Cake mai tabin strawberry
Wannan cake asali wajen Maryama's kitchen na ganshi ta yi cupcake da recipe din.
Na yi qare-qare a nawa, kamar na kala da cream....amma dai gaba daya yabawar tata ce.
Na yi girkin ne tun watan agustan 2020,dalilin kwadayi irin na lokacinnan na wata😁cikin dare har na kwanta na tashi na yi,ban samu damar daurawa ba sai yanzu.....
Babbar sadaukarwa ga Bint's Cuisine💕 Da Maman Jafar🤗💕na gode muku na kuma yi kewarku da cookpad duka.
Umarnin dafa abinci
- 1
Na fara da hada sukari,mai da kwai cikin blender na markadashi na minti 5
- 2
Sai na juyeshi a wani kwanon,na zuba flavor kana na tankade fulawa da bakar powder tare na cakudesu a hankali,sannan na saka kala(ta abinci)shudi
- 3
Sai na samu kaskon gashi na shinfida takarda ta gashi na juye qullin cake dina na gasa shi wutar sama da qasa 15f
- 4
Na ajiyeshi ya huce(da dare na yi sai da safe na hada cream din). Na hada whipping cream da madarar hollandia na yi amfani da whisker na kadashi bai kama jikinshi da kyau ba
- 5
Na yayyanka cake din fasalin square ina shafawa daya sai in dora daya a kai har na gama duka sai na shafe jikinshi duka da shi na murmusa sauran cake din a kai na saka a fridge ya yi sanyi
- 6
Babana da ba ya son zaqi ma ya ci har da guzuri da shi zuwa Zaria😅
Cooksnaps
Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!
Similar Recipes
-
-
Ice cream din ayaba me almond
Na yi shi ne sanda akayi gasar ice-cream kasancewar na tashi da gjy ranar ban wallafa ba sai yanzu. #kano Khady Dharuna -
-
Kitsattsen dublan
#FPPCNaga wannan girki tun wajen watanni 9 baya a wajen princess amrah lkcn ana cikin gasar dublan ya bani sha'awa amma sai nk jin kmr zai bani wahalar yi😩sai ynx na tattara qarfin gwiwar gwadawa......gashi dai bai samu wani hoton kirki ba amma muna godiya da gudummawarta garemu❤💥 Afaafy's Kitchen -
Lemon moctail na shudin (blue)curacao 😫💃
Wannan lemo na musamman ne da labarin qayatarwarshi ya samo asali daga wjn yar uwa ta musamman....Maryama's kitchen ♥️ Afaafy's Kitchen -
Peanut burger 2
Na Yi order ne a wajen moon, kamar da Wasa yara sukace nayi ta siyarwa nace tom, aikuwa a kwana 1 ta kare gashi munada nisa, Tana kaduna Ina Kano☹️🤦 ba shiri na tashi nayi na zuzzuba kamar dai yanda ta aikon da shi. #wearetogether Khady Dharuna -
Chocolate da red velvet cake
#nazabiinyigirkiCake nau'i ne na kayan zaqi da ake cewa dessert da turanci. Ana cinshi bayan an gama cin abinci mai gishiri da a samu daidaiton dandano a harshe kuma suna da dadi sosai,sannan ana yinsu dandano daban daban. Na yi wannan cake din ne wa kaina da sauran 'yan gdanmu, amma mu ma ba qa'ida muke bi ba😂mun ji dadinshi sosai.Bayan an gama gasa cake din kamar yadda na yi bayani a qasa kar a yi garajen cireshi daga gwangwani a take, a barshi ya gama hucewa gaba daya dan gujewa fashewa. Afaafy's Kitchen -
Kosai mai zogale
#kosairecipecontest.Saboda amfanin zogale a jikin dan Adam kama daga maganin gyambon ciki,typhoid da malaria na zabeshi domin ya zamo ganye cikin sinadaren da zanyi amfani dashi a cikin wannan girki nawa. Kwai da bakar hoda na kara wa kosai laushi da ke bayarda dadi na musamman.Dalilin wannan a koda yaushe na ke cike da marmarin kosai ba tare da gimsheni ba.Da fatar mai karatu zaya ji dadinsa bayan biyar wannan hanyoyin da zanyi bayani akai domin sarrafa kosai.Ayi girki cikin nishadi. fauxer -
Kwalliyar donut(strawberry flavor)
Abu ne me matukar daukar hankali da kyau,bugu da kari,ga uwa uba dadi Fulanys_kitchen -
Dalgona cookies
Wannan biskit na yishi ranar farko da aka saka dokar hana fita a kano.Da farko nayi niyyar yin dalgona coffee ne wanda ake yayi a daidai lkcn,to gsky lokacin zuciyata bata kwanta da yinshi ba saboda ina tunanin zai yi daci,har na fara sai kuma na canza ra'ayina zuwa biskit saboda dama nayi kewarshi kwana biyu,nayi amfani da nescafe din da na buga ne da sauran butter cream da nayi amfani dashi kwana hudu kafin yin biskit din #FPPC Afaafy's Kitchen -
Classy Cincin
Na kasance Ina son cincin tun Ina karama na taso Naga mamana tanayi, cincin kala kala babu wnada bnaga tayi ba. Yanzu Nima alhamdulillah zamani yazo da cigaba mukan taba yin me Dadi da kaayarwa. Wannan dai na saka Masa lemon zest wato bawon lemon Zaki/tsami. Dandanonsa dabanne, Yana kwana Yana dada Dadi😍😋😋😋 Khady Dharuna -
Butter chicken
Wannan girki ya samo asali ne daga arewacin qasar hindu tun wajejen shekarun 1950s. Manyan kayan hadinshi shi ne kaza,butter da tumatur, sauran duk qari ne dan fito da dandano na musamman. Na yi wannan girki ne domin kaina. Na tashi tun ina yarinya dalilin kallon fina-finansu na fara sha'awar al'adunsu, yarukansu da abincinsu, wannan yana daya daga cikin abincinsu da nake matuqar so. Afaafy's Kitchen -
Strawberry milk shake/ ice cream
Wannan hadin zaki iya barinsa yayi kankara kimaidashi ice cream zakuma ki iya shansa a haka Meenat Kitchen -
-
Biskit mai kostad(custard)
Na kasance ina yawan ganin hanyoyin yin biskit a gurin jahun delicacies,har ya kasance da zarar naga an turo girkin biskit to nasan itace🙄amma fa banda yanzu domin kuwa bata ajiye baiwar a tare da ita kadai ba,ta koya mana kuma muna qoqarin gwadawa🤗mun gode Aunty Sadiya. Afaafy's Kitchen -
-
Vanilla cake
Yanada dadi sosai musamman inkanasha da lemo mutane nasan vanilla cake sosaiRukys Kitchen
-
Buns din da ake zuba nutella a ciki mai kirar catapillar
A duk sadda na so in canza kalacin safe nakan yi wannan biredin, in ci shi da zafinshi akwai dadi sosai. Princess Amrah -
Hanjin ligidi
#alawa 😋Hanjin ligidi shine alawa mafi soyuwa a gareni tun lokacin yaranta🤗har yinta nakeyi ina sayarwa a lokacin da nake firamare shi yasa ma yanzu da na ci karo da gasar alawa nace to bari in tuna baya.Yayi dadi sosai😋 #alawa Hauwa Rilwan -
-
9ja map cake
Nigeria kasata abin alfaharin mu ina murna da kata ta samu yancin kanta daga turawan mulkin mallaka @59 #oct1st Sumieaskar -
Pan cake
#myspecialrecipecontest wannan shi ne karon farko da na gwada yin pan cake, sai dai abun mamaki ko kadan bai bani wata gardama ba. Ya tafi daidai yadda na so tafiyarshi har ma ya zarce. Ya yi kyau a ido sannan ya bada dandano mai matukar dadi a baki. Ku gwada tawa hanyar yin pan cake din na tabbata za ku gode min a karshe. Princess Amrah -
Pizza cake
#team6cake. A kullum kokari nake naga na samo hanya sarrafa abubuwa, ta hakane na samu sarrafa cake a matsayin pizza. Afrah's kitchen -
Kek mai chakulet (chocolate cake)
Ina godiya sosai ga Chef Suad da kokarinta wurin ganin ta koyar da mu wannan kek kuma mun koya. Hakika en gidanmu kowa ya ji dadinsa suna burin in sake yi musu irinshi. Na gode sosai Princess Amrah -
Cookies
Cookies nada kyau a rikayima Yara surika zuwa dashi makaranta, ko Kuma Wani event idan yatashi, Kai ba Yara kadaiba hadda manya Mamu -
Cookies
Godiya me yawa gareki sadiya jahun , ta dalilinki na koya cookies kala kala Allah ya saka miki da alkhairi bana cikakken Sati banyi shi agidana ba kowa yana jindadinshi. Afrah's kitchen -
-
Wainar Filawa
Tun safe na tashi da kwadayin wainar filawa kuma banda isashen lokaci na dawo ta school late Amman nace koma yayane se nayi,Alhamdulillah na samu nayi kwadayi ta koma💃 Ashley culinary delight -
Mango Panna Cotta
Ni ba maabociyar shan mangoro bace. Na yi shine domin iyalina kuma sun sha sun yaba sosai har suna fatan na sake yi musu irinshi. Princess Amrah -
More Recipes
sharhai (4)