Pan cake

Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
Kaduna

#myspecialrecipecontest wannan shi ne karon farko da na gwada yin pan cake, sai dai abun mamaki ko kadan bai bani wata gardama ba. Ya tafi daidai yadda na so tafiyarshi har ma ya zarce. Ya yi kyau a ido sannan ya bada dandano mai matukar dadi a baki. Ku gwada tawa hanyar yin pan cake din na tabbata za ku gode min a karshe.

Pan cake

#myspecialrecipecontest wannan shi ne karon farko da na gwada yin pan cake, sai dai abun mamaki ko kadan bai bani wata gardama ba. Ya tafi daidai yadda na so tafiyarshi har ma ya zarce. Ya yi kyau a ido sannan ya bada dandano mai matukar dadi a baki. Ku gwada tawa hanyar yin pan cake din na tabbata za ku gode min a karshe.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Flour kofi daya da rabi
  2. Sugar cokali babba biyu
  3. Kwai guda biyu
  4. Narkakken butter 1/4 kofi
  5. Baking powder karamin cokali biyu
  6. Baking soda. Karamin cokali daya
  7. cokaliGishiri rabin karamin
  8. Madara kofi daya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ga abubuwan bukata

  2. 2

    Ki zuba flour a wani kwano daban, sai ki zuba sugar da baking powder

  3. 3

    Ki zuba baking soda da gishiri ki motse sosai. Kin hada busassun kayan hadin kenan.

  4. 4

    A wani kwanon daban kuma sai ki fasa kwai, ki zuba madara da narkakken butter ki motse su sosai. Jikakkun kayan hadin kenan

  5. 5

    Ga su nan sai ki motse sosai.

  6. 6

    Sai ki zuba jikakkun kayan hadin a cikin busassun.

  7. 7

    Ga shi nan bayan na motse. An gama kwa6i kenan

  8. 8

    Ki zuba mai kadan a cikin kasko (non stick)

  9. 9

    Sai ki yi amfani da 1/4 kofin awo ki zuba shi sau biyu. Sannan ki bubbuga kaskon a hankali don ya baje.

  10. 10

    Idan ya fara fitar da kwayaye sai ki juya dayan gefen. Bayan kin tabbatar ya yi ki sauke.

  11. 11

    Ga shi nan na gama

  12. 12

    😍😘

  13. 13

    A nan kuma sai na zuba nutella a kai

  14. 14
  15. 15
Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
rannar
Kaduna
I absolutely love cooking. I can merrily state that my kitchen is my playground in every sense! My mother has always been a wonderful cook, and I feel she is my inspiration.
Kara karantawa

Similar Recipes