Wainar masa

UH CUISINE
UH CUISINE @Bint_nuh
Kano State Nigeria

Abincin hausawa mai dadi da inganci zaka iya yin karin kumallo dashi ko kuma aci da rana. Hausawa nason wainar masa shiyasa da wuya ayi taro biki ba'ayita ba. Ana iya sarrafa qullin zuwa wani abincin wanda aka fi sani da sinasir.

Wainar masa

Abincin hausawa mai dadi da inganci zaka iya yin karin kumallo dashi ko kuma aci da rana. Hausawa nason wainar masa shiyasa da wuya ayi taro biki ba'ayita ba. Ana iya sarrafa qullin zuwa wani abincin wanda aka fi sani da sinasir.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

24hrs
10-15 peoples
  1. Farar Shinkafa (ta tuwo) kofi takwas
  2. Dafaffiyar Jar shinkafa kofi daya
  3. Yeast cokali biyu
  4. Baking powder karamin cokali daya
  5. Sugar quater
  6. Gishiri cokali daya
  7. Citta (optional)
  8. Albasa guda daya
  9. Mai cup 2

Umarnin dafa abinci

24hrs
  1. 1

    Da farko zaki samu farar shinkafa ki wanke ki jiqata tayi 6hours

  2. 2

    Idan ta jiqu seki zubar da ruwan ki zuba dafaffiyar shinkafar ki da yar citta seki kai markađe.

  3. 3

    Idan an markado seki juye a mazubi babba me murfi(hikimar haka saboda idan ta tashi kar ta zube) seki zuba yeast dinki kirufe kisaka a guri mey dumi kibarshi yayi 6hrs.

  4. 4

    Bayan nan qullinki ya tashi seki zuba baking powder ki sugar, da gishiri ki juya ki tabbatar kome ya hade.

  5. 5

    Seki dora tandarki a kan wuta ki zuba mai cokali daya a kowane rami ya danyi zafi se a zuba qullin wainar a kowane rami seki Dan barbađa albasa akai idan ta soyu sai ki juya.

  6. 6

    Za'a chi da miyar taushe ko miyar agushi za kuma iya ci da kuli-kuli ko zuma ko sugar.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
UH CUISINE
UH CUISINE @Bint_nuh
rannar
Kano State Nigeria
Ummahani Nuhu Abdullah aka UHNA. Food scientists i love food and i like cooking food...APPETIZERS🍖 MAIN DISH🍛 &DISSERT🍨... Setting menu,table cover🍴🍷table accompaniment & food accompaniment 🍲🍗🍹🍻🍟.... i like watching food channels and new recipes....💞✨
Kara karantawa

sharhai (4)

Similar Recipes