Yadda zaki yi wainar semovita da miyar alayyahu

Ummu ashraf kitchen
Ummu ashraf kitchen @cook_19629121
Kano

Wainar semovita tana da dadi sosai ga laushi,ga kuma sauki wajen sarrafata

Yadda zaki yi wainar semovita da miyar alayyahu

Masu dafa abinci 7 suna shirin yin wannan

Wainar semovita tana da dadi sosai ga laushi,ga kuma sauki wajen sarrafata

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 1 kgSemovita
  2. Dafaffiyar farar shinkafa(cup 3)
  3. Sugar,salt
  4. Yeast,baking powder
  5. Kayan miya
  6. Maggi,onga,curry,mai
  7. Alayyahu
  8. Albasa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki samu babban kwano mai kyau ki zuba semovita aciki kisa yeast,sugar,da gishiri kadan ki juya saiki zuba ruwan dumi ki kwabashi kaurin sa kamar na koko saiki dakko daffafiyar shinkafarki ki zuba ki kara juyawa sai ki rufe ki barshi ya tashi,idan ya tashi saiki yanka albasa madaidaita aciki kisa baking powder ki juya idan yayi danyi ruwa ki kara semovita aciki dan so ake yayi kauri sosai yadda bazai yi ruwa ba saiki soya a tanda.

  2. 2

    Yadda zaki hada miyar allayyahun ki,da farko zaki wanke kayan miya ki markada ko kiyi grating dinsu,ki zuba a tukunya ki dura a wuta ya tafasa idan ya tafasa saiki sa mai,maggi,onga,da sauran kayan kamshi saiki juya ki barshi kamar minti 5 saiki zuba allayyahunki da kika yanka da albasa ki juya saiki rufe kibarshi ya turara zaki ji kanshi yana tashi saiki kashe.aci dadi lafiya.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ummu ashraf kitchen
Ummu ashraf kitchen @cook_19629121
rannar
Kano
I luv cooking
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes