Tuwon alabo da miyar alayyahu

Maijidda Musa
Maijidda Musa @cook_16773230
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Alabo
  2. Alayyahu
  3. Albasa
  4. Maggi
  5. Kifi
  6. Man ja
  7. Attaruhu gishiri domin Dandanan miya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki samu Alayyahunki ki gyara ki tsinke ki cire mara kyau ki yanka sannan ki wanke da ruwan zafi sbd kwayoyin cuta

  2. 2

    Sannan ki gyara albasa da attaruhu ki wanke ki jajjaga tare sai ki daura manjanki a wuta ki soya sai ki kwashe albasar ki zuba jajjageggen kayan miyarki ki soya sannan ki zuba magginki da kifinki ki cigaba da soyayya kamar miti sha biyar sai ki saka Alayyahunki ki suya karki rufe zai haifar miki da ruwa kiyi ta juyawa har komai yayi dai dai sai ki samu kawonki ki juyea

  3. 3

    Sai ki samu alabonki ki tankade ki daura ruwa Akan wuta in ya tafasa sai ki rage ruwan ki sauke kasa sai kina zuba garin kina turawa in yayi yarda kike so sai kimayar kan murhun kina juyawa ko ma biki mayar ba ba mtl in yayi tauri zaki iya kara ruwan zafi shine dalilin da ake rage ruwan ki kin gama miyarki ta Alayyahu soyayye da tuwon alabo sai ci

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Maijidda Musa
Maijidda Musa @cook_16773230
rannar

Similar Recipes