Tura

Kayan aiki

2hrs
20 yawan abinch
  1. Shinkafa
  2. Ruwa
  3. Kabewa
  4. Kayan miya
  5. Man ja
  6. Man kuli
  7. Alayyahu
  8. Sinadarin dandano
  9. Kayan Kanshi
  10. Nama
  11. Yankakkiyar albasa

Umarnin dafa abinci

2hrs
  1. 1

    Ki dora tukunya a wuta ki zuba ruwa in ya tafasa ki zuba shinkafar (zaki wanke ta ki rege sannan ki tsane ta) kada ki cika mata wuta ki barta ta dahu sosai sannan ki sa muciya ki tuka(idan ya danyi ruwa se ki daure shi da garin semovita sannan ki rufe ya turara.amma ba'a so yayi tauri sosai) in yayi ki sauke ki kuma tukawa sannan ki saka mara ki kwashe kina sawa a leda ki mulmula se ki nade.

  2. 2

    Ki wanke naman ki zuba a tukunya ki sa albasa,kayan kanshi, sinadarin dandano da dan gishiri se ki zuba ruwa kadan ki dora a wuta ki dafa shi sosai.in ya dahu ki soya shi sama sama.
    Ki gyara alayyahun ki yanka se ki wanke shi da gishiri sannan ki tsane

  3. 3

    Ki gyara kayan miyan ki wanke sanan ki markada se ki dora shi a wuta ki dafa.ki feraya kabewar ki wanke ta ki zuba a tukunya ki zuba ruwa se ki dafa in ta dahu ki juye a blender ki markada.

  4. 4

    Ki zuba man ja da na kuli a tukunya ki zuba albasa da Jajjagaggen citta da tafarnuwa ki soya su sannan ki kawo wannan naman ki zuba ki cigaba da juyawa minti 3 se ki zuba dafaffan kayan miyan ki soya su sannan ki kawo dafaffan kabewar, sinadarin dandano da kayan kanshi ki zuba ki juya sannan ki rufe ya dahu sosai amma fa kada kisa wuta da yawa.in ta dahu se ki zuba alayyahun da yankakkiyar albasa ki rufe minti 3 se ki kashe wutar ki juya miyar.

  5. 5

    Zaki iya kara ruwa in kaurin yay miki yawa

  6. 6

    Shi kenan aci dadi lpia 😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ummu Aayan
Ummu Aayan @Sadiyanahajakitchen
rannar
Kano

sharhai (4)

Maman jaafar(khairan)
Maman jaafar(khairan) @jaafar
Masha Allah da fatan anyi sallah lafiya

Similar Recipes