Wainar Fulawa

sadiya bako
sadiya bako @LeemcykhanCuisine

Sadiya Bako

Tura

Kayan aiki

  1. Fulawa Kofi biyu
  2. Kwai guda daya
  3. Tarugu 5
  4. Albasa 1
  5. Mangyada
  6. Maggi 1
  7. gishiri
  8. Ruwa yadda zai isa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki tankad'e fulawar a mazubi mai kyau,sai ki d'auko jajjagaggun attarugu da albasan ki kizuba akan fulawar ki,ki d'auko Maggi da gishiri ki zuba,ki kawo ruwa ki zuba ki juya sosai,

  2. 2

    Sannan ki kawo k'wan ki ki xuba,kisa maburgi ko whisk juya sosai ya zama babu gudaji,

  3. 3

    Sannan Kar yayi kauri kuma kada yayi ruwa.

  4. 4

    Daganan kisa kasko a wuta yayi zafi kisa mangyada idan yayi zafi,

  5. 5

    Sai ki samu ludayi madai daici ki dinga diban kullun fulawar ki,kina zuba wa a kasko idan gefe daya yayi sai ki juya gefen

  6. 6

    Note:zaki iya soya wa da manja basai mangyada kadai ba

  7. 7

    Idan ya soyu sai cire kisa a plate.Haka zakiyi tayi har kullun ki ya kare, shikenan kici kayanki da yaji idan kinason yaji

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
sadiya bako
sadiya bako @LeemcykhanCuisine
rannar

Similar Recipes