Ingredients

  1. Tsamiya me kyau
  2. Sugar
  3. Ginger
  4. Barkono, kanumfari
  5. Cucumber

Cooking Instructions

  1. 1

    Da farko xaki wanke tsamiyan ki, ki saka ta a tukunya, ki goga ginger dinki da greater ko ki daka itama ki xuba a tukunyar ki kawo dan barkonon ki kaman 5pcs ki xuba da kanumfarin ki, ki xuba ruwa a tukunyar ki daura a wuta ki rufe ya tafasa, ki sauke ki ajiye a gefe. (Make sure ginger din dayawa sabida anaso a danji yaji yaji)

  2. 2

    Sai ki samu pan dinki haka, ko wanda bakya amfani dashi sai ki kawo sugar dinki ki xuba a pan din ki daura a wuta ki barshi har sai yayi baki saiki sauke ki xuba mishi ruwa. Ki ajiye a gefe.

  3. 3

    Sai ki dauko cucumber dinki kaman guda 1 ki yayyanka ta ki saka a blender ki markada ta ki tace ki ajiye ruwan a gefe.

  4. 4

    Sai kixo ki dauko tsamiyan da kika dafa ki tace da rariya me laushi sosai, kinayi kina dauraye tsamiyan kina kara tacewa har ki gama tacewa tsaf, sai ki kawo sugar dinki ki zuba, ki kawo cucumber juice din nan naki shima ki xuba, sai ki kawo ruwan konannen sugar din nan shima ki xuba. Ki jujjuya sosai in kinji da dan tsami saiki dada kara ruwa, shi wannan ruwan konannen sugar din kaman color ne da xai bawa juice dinki, shikenan kisa a fridge yayi sanyi in kin tabbata komai yayi daidai.

Reactions

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan

Comments

Written by

Al-marash_cuisine
Al-marash_cuisine @cook_18681358
on
Kano
i'm maryam alhassan aliyu, B.sc.physics . i have so much passion in cooking.
Read more

Similar Recipes