KFC Chicken

mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
Kaduna State, Nigeria

Wannan suyar kazan yana da dadi kuma wani canji ne na soya kaza ba yadda aka saba yau da kullun ba.

KFC Chicken

Wannan suyar kazan yana da dadi kuma wani canji ne na soya kaza ba yadda aka saba yau da kullun ba.

Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. 4parts Kazan agric
  2. Marinade:
  3. Gishiri daidai bukata
  4. 1Ginger garlic paste chokali babba
  5. 2Buttermilk kofi
  6. Coating:
  7. 1Flour kofi
  8. 1Kwai
  9. Cornflakes 1/4 kofi
  10. Oregano 1/2 karamin chokali
  11. Madara1/4 kofi
  12. Gishiri yadda ake bukata
  13. Masoro 1/2 karamin chokali(dakakke)
  14. Mixed herbs1/2 karamin chokali
  15. Tarugu yadda ake bukata
  16. Albasa madaidaiciya
  17. Mai na suya

Cooking Instructions

  1. 1

    Da farko ki hada kayan marinade dinki a roba meh zurfi idan baki da buttermilk seh ki hada madara da vinegar ko lemun tsami chokali 2 ki barshi tsawon minti 10 ko 15 seh kiyi amfani da shi. Sai ki saka kazan cikin hadin ki rufe ki barshi yayi kaman awa 3 ko 4 ko ki barshi ya kwana cikin fridge.

  2. 2

    Ki samu wani roba ki zuba kwai, gishiri,madara ki kada ya hade seh ki aje gefe.Cikin wani roban kuma ki sa flour,gishiri,ki marmasa cornflakes ki zuba ciki,masoro,oregano,mixed herbs ki juya sosai ki aje gefe.

  3. 3

    Ki dakko kazar da kika sa cikin marinade ya tsumu seh ki tsame ki sa a tukunya ki sa albasa da tarugu da dandano seh ki dora kan wuta amma kar ki sa wuta da yawa kuma kar ki zuba ruwa.ki na yi kina dan girgiza tukunyar saboda kar ki juya ya fashe.idan ya dan kame jikinshi seh ki sauke kar ki barshi ya sha wuta kar ya fashe.ki tsane shi a colander ya huce.

  4. 4

    Idan ya huce seh ki na daukan naman daya bayan daya kina sawa cikin hadin flour ki bade shi ko ina yaji hadin seh ki aje a plate har ki gama.

  5. 5

    Idan kin gama seh ki sake dauka daya bayan daya wanda kika sa cikin hadin flour ki tsoma cikin hadin kwai ki sake sawa a cikin hadin flour seh ki aje a plate

  6. 6

    Idan kin gama gaba daya seh ki dora mai a wuta idan yayi zafi seh ki soya.

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
on
Kaduna State, Nigeria

Comments

Similar Recipes