Gashasshen Dankalin Turawa
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko xaki fere dankali ki yankashi round... Seki dauko tukunya kizuba ruwa kizuba dankalinki aciki da gishiri kadan dakuma turmeric seki daura a wuta har tsawon minti 15.
- 2
Kiyanka catfish dinki xuwa gida 4-6 kijiqa a ruwa kamar minti 5..seki wanke ki tsame a matsami
- 3
Ki jajjaga kayan miyanki tare da danyar citta, tafarnuwa da cardamon
- 4
Ki tsame dankalinki a matsami seki dauko roba kijuye, ki dauko wankekken catfish dinki kijuye, kijuye kayan miyanki, kizuba maggi, onga, coriander da albasa... Ki juya da ludayi ya hadu sose, seki juye a foil pepper...
- 5
Ki dauko hadin ki sakashi a oven na tsawon minti 10-15 seki fito dashi.... Aci lafiya
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/10560636



sharhai