Sinasir na Semovita
Wannan girki yanada dadi kuma ga sauqin yi...Agwada aci dadi
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko xaki xuba garin semovita dinki a roba
- 2
Kikawo yeast kixuba sannan kizuba ruwa kikwabashi,saikisa a waje mai dumi yatashi
- 3
Idan yakumburo yai bulali saiki xuba sugar daidai yadda kikeso da gishiri kadan da albasa da dan attarugu kadan kijujjuya
- 4
Saiki dauran kaskon suya awuta kisa mai kadan kibari yadanyi xafi
- 5
Kidebo qullun kixubashi yai fadi kuma kada yacika kauri
- 6
Kisa murfi kirufe kirage wuta
- 7
Idan yai saqa yasoyu saiki kwashe
- 8
Zaa iyacinshi da miyar Taushe kokuma hakanan ko da yaji
- 9
Aci dadi lafiya
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11082750




sharhai