Umarnin dafa abinci
- 1
Za'a sami wake a zuba ruwa yayi kamar minti biyar sai a zuba a turmi a surfa shi sannan a wanke a fitar da duk dusar tsaf.
- 2
Idan an gama gyara waken sai a wanke a yanka albasa a hada da Attaruhu a markada yayi laushi sannan ba'a so yayi ruwa.
- 3
Idan an markada za'a sami ludayi a buga shi sosai har ya tashi sai a zuba gishiri dai-dai dandano.
- 4
Za'a zuba mai a kaskon suya a dora a wuta idan yayi zafi sai a sa cokali ana dibar kullin waken ana sawa a mai ana soyawa.
- 5
Za'a iya cin kosai da kunu ko da koko ko da shayi da Bread.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11981153






sharhai