Ring Samosa

Meenat Kitchen
Meenat Kitchen @meenat2325
Kano State

Nau ine na sarrafa kalolin snacks kada wadancn su ginsheka

Ring Samosa

Nau ine na sarrafa kalolin snacks kada wadancn su ginsheka

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

30mintuna
3 yawan abinchi
  1. Flour Kofi biyu
  2. Mai cokali 4
  3. Sugar cokali daya
  4. Gishiri karamin cokali daya
  5. Fillings
  6. Minced meat
  7. Albasa da attarugu
  8. TafarnuwadA sindarin dandano
  9. GIshiri,curry,kayan kamshi
  10. Mai

Umarnin dafa abinci

30mintuna
  1. 1

    Dafarko ki fara gyara namanki ki dorasa a wuta ki yanka albasa kisa kayan kamshi da maggi da gishiri kibarshi ya dahu

  2. 2

    Idan ya dahu ki jajjaga attarugu da tafarnuwa ki zuba akai kisa mai da curry ki soyashi sama-sama ki kwashe kisa a bowl

  3. 3

    Saiki dauko hadin sama na dough ki kwaba dough dinki,saiki rufe kibashi mintuna 5-10 saiki raba flour din 6 saiki dunga daukar one by one kina murzata da fadi

  4. 4

    Idan kin gama murzawa saikisa wuka ko pizza cutter ki yanke gefe da gefe ki maida ita square wato kwana 4 equal saiki dauko hadin namanki kisa a sama saiki Dan matso da naman kasa amma kada yakai tsakiya saiki shafa kwababbiyar flour ki dauko saman ki rufe namanki shima kada kibari kici Rabin flour dinki saiki dauko wuka ko pizza cutter ki dunga tsaga flour din daga daidai inda kika rufe zuwa kasa

  5. 5

    IDan kin gama yankawa saiki shafawa karshen kwababbiyar flour saiki nade flour dinki kamar tabarma saiki dauko gefe da gefen dake bude ki shafawa bangare daya kwababbiyar flour saiki mannesu tare zakiga ya baki kamar zobe shikenn kin gama saiki Dora mai a wuta idan yayi zafi ki soya till golden brown.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Meenat Kitchen
Meenat Kitchen @meenat2325
rannar
Kano State
my name is Amina Mohd Sani, cooking is my fev,cooking is my hubby......
Kara karantawa

sharhai (11)

Syeda Sarah Taha
Syeda Sarah Taha @ST_Kitchen123
Asalam u alaikum wrb dear
Ramadaan Kareem
Thanks for sharing
Love from Pakistan

Similar Recipes