Alalle da veggies sauce

Alalle da veggies sauce
Umarnin dafa abinci
- 1
Idan kika wanke waken Sai ki markade shi da tattasai da attaruhu kar yayi ruwa sosai Sai kisa mai maggi da gishiri da hantan ki da kin riga ki dafa kin yanka ta kanana ita da Kwai sai ku zuba su a ciki, Sai ki soya manjan ki zuba shima a ciki sai ki zuba yankaken albasa a ciki ki juya shi Sai ki kulla shi a leda
- 2
Sai kisa ruwa kadan a tukunya ki zuba alallen a cikin ki rufe shi da leather Sai kisa marfin tukunya ki barshi ya dahu idan kikaga leathern ya rabu da alallen toh yayi kenan
- 3
Sauce din kuma zaki zuba mai kadan a tukunya da albasa idan yayi zafi sai ku juye naman da kika tafasa kika yanka kanana ki soya shi idan ya kusa soyuwa sai kusa attaruhu da tattasi da grean pepper da carrot din ki juya Sai kisa maggi da ruwa dan kadan saboda maggin ya dahu idan yayi kaman 2mints Sai ki juya zaki ga ruwan ya kusa karewa Sai ki zuba cabbage din a ciki ki juya ki bashi 1mint Sai ki kashe
Keywords
Similar Recipes
More Recipes





sharhai