Masar shinkafa da miyar alaiho mai gyada

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Yana da dadi sosai musamman lkcin karya na safe

Masar shinkafa da miyar alaiho mai gyada

sharhi da aka bayar 1

Yana da dadi sosai musamman lkcin karya na safe

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafar tuwo kofi biyar
  2. Yeast chokali biyu
  3. chokaliBaking powder rabin
  4. Sugar kofi daya
  5. Gishiri dan kadan
  6. Flour kofi daya
  7. Hadin miya
  8. Alaiho
  9. Attarugu
  10. Tumatur
  11. Albasa
  12. Maggi da sauran sinadaran dandano
  13. Curry da thyme
  14. Nikakken gyada
  15. Nama da bandan kifi
  16. Tafarnuwada citta
  17. Mai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki wanke shinkafarki da kyau sannan kidibi kadan kamar kofi daya kidafa sauran kuma kijika shi kamar zuwa awa daya haka sai ki tsane ruwan sannan ki dauko wanda kika dafan ki hadasu tare ki jujjuya sai ki kai anika miki ita

  2. 2

    Bayan kin nika sai ki jujjuyashi sosai sannan kizuba sugar gishiri da fulawa ki jujjuya sosai sannan kizuba yeast da baking powder kisake jujjuya sosai komai yahade sai kirufe kibarta don yatashi

  3. 3

    Hadin miya---zaki yanka alaiho sannan kizuba gishiri kiwanketa sosai tayi fes sai kizuba a colander ki ajiye agefe don ruwan tatsane. Sai kiyanka albasa ki yanka tumatur ki jajjaga tafarnuwa da citta duk ki ajiye agefe sannan kisake jajjaga attarugu shima ki ajiye age

  4. 4

    Sai kidaura tukunya akan wuta kisa mai idan yayi zafi sai kizuba albasa kisoya bayan albasa yasoyu sai kizuba tafarnuwa da citta ki jujjuya sannan kizuba tumatur sai kisa tafasasshen namanki ki jujjuya sai kizuba su maggi da sauran sinadaran tareda curry da thyme kisake jujjuyawa sannan kidauko attarugu kizuba sai kidan juyata sannan kibarta yasan soyu yanda komai zai shiga jikin naman

  5. 5

    Sai kidauko ruwa dan daidai kizuba akai kijuyashi sannan kigyara kifinki da kyau yanda zakicire duka kayar sannan kiwanketa sosai sai kizuba akai kijuyashi sai kirufe kibari

  6. 6

    Bayan yatafasa sai kizuba gyada kidan jujjuyashi sai ki rage wutan sannan kidauko alaihon kizuba akai ki jujjuya sai kirufe kibarta idan yanuna sai kisauke

  7. 7

    Sai kiduba kullin masan idan yatashi sai kidauko kaskon masanki kidaura a wuta kisa mai kadan kadan akowanne idan yayi zafi sai kidiba kullin kizuzzuba a ko wanne kibarta idan dayan bangaren yayi sai kijuya dayan gefen shima yayi sai kocire. Haka zakiyi tayi har kigama

  8. 8

    Shikenan aci dadi lfy

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

Similar Recipes