Dambun tsakin masara
Dadin ba'a magana
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko a gyara tsakin masarar a wanke shi tas a tsaneshi, sai a samu madambaci ko colander a zuba a ciki a dora a wuta adan turara
- 2
A tsinke zogale a wankeshi ya tsane, a jajjaga attaruhu a yanka albasa, a daka gyada a bushe ta adan kuma daka ta
- 3
Inya dan turaru sai a sauke, a zuba zogale, attaruhu, albasa, gyada, gishiri, dandano, spices, curry, sai adan zuba man gyada a tona sosai ko ina yaji.
- 4
Sai a mayar madanbaci ko colander a barshi ya karasa dahuwa.
- 5
Shikenan inya dahu zaaji yana kamshi sosai kuma kayan ciki sunyi laushi sai a sauke
- 6
Wasu na ci haka, wasu kuma na kara mai da dakakken yaji, aci dadi lfy.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/12251409




sharhai (2)