Awara
Wanan abinci nayi shi ne domin na burge maigina kuma yaji dadin
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki yanka karas dinki bayan ki wanke shi sai ki yanka albasa itama da lawashinta
- 2
Bayan nan sai ki kawo mai ki zuba a tukunya idan yayi zafi ki zuba kayan miya ki soya su kisa maggi da kayan kamshi
- 3
Bayan nan kuma sai ki kawo karas da albasa ki zuba ki soya su kadan sanan ki kawo awarar ki zuba ta ki juya ko ina ya hade
- 4
Bayan minti kamar biyu sai ki sauke kisa lawaashi ki yanka sama zaa iya ci haka ko da shinkafa ko taliya
- 5
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/15680947









sharhai (7)