Cake gashin gargajiya

Zakiyi shi as snacks ne, zaa sha da tea ko lemu
Cake gashin gargajiya
Zakiyi shi as snacks ne, zaa sha da tea ko lemu
Umarnin dafa abinci
- 1
Ki hade flour baking powder da madara waje daya ki jujjuya
- 2
Zaki buga butter sugar da mai na minti 5-7 har ya ninka adadin sa (double in size)
- 3
Zaki raba kwanduwar kwai da farin, kiyi blending farin ko kisa a mixer ya bugu sosai.
- 4
Zaki zuba kwaduwar da kika kada a cikin sugar da butter din da kika buga no
- 5
Zaki zuba Rabin hadin flour a cikin hadin butter da sugar da mai da kwanduwar
- 6
Zakiyi folding ba jujjuyawa ba, sai ki zuba Rabin farin kwai da kikayi blending
- 7
Kiyi folding shima, sai ki juye ragowar flour ki yi folding shima
- 8
Zaki juye sauran farin Kwan kiyi folding, shikenan batter dinki ya hadu.
- 9
Zaki sami baking pan ko trar ki shafa butter ki barbada flour ko ki shafa mai ki barbada flour sai ki zuba a ciki.
- 10
Zaki zuba kasa a tukunya ki saka wani karfe sai ki dora pan din idan kasar tayi zafi ki dora ki rufe ruf amma kisa wuta kadan
- 11
Baa cikawa sabida yana tasowa kuma sabida yayi gashi me kyau, kada kasan ya gasu tsakiya danye, kada kafin sama ya gasu kasan ya kone
- 12
A karshe cake ya gasu, min 20-25 zai gasa miki shi, wannan adadin pan 4 yayi min, amma kina gashi yana kara zafi ba lallai na karshe ya Kai minti 20 ba watakila ma minti 15 ya gasa miki biyun karshe. Laushin sa kamar sponge cake.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes























sharhai (2)