Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko zaki samu robanki mai dan fadi,seki kawo fulawarki wanda kika tankade seki sanya acikin roban,seki kawo bakin hodanki rabin cokali karami seki zuba akan fulawar,seki kawo suganki cikin cokali na cin abinci ki zuba cikinsa biyar,seki gauraya sannan ki zuba man gyadanki cokali hudu seki fasa kwan ki ki zuba akai seki gauraya domin ruwan kwan ni shine ruwana domin ya isa amma inkinga bai hada jikinsaba to seki kara zuba ruwa harsekinga ya hadu da tauri ake kwabashi yar uwa,seki rufe
- 2
Kibashi kamar minti biyar,seki sake dan mammatsawa seki yanka,yankan dakikeso,seki daura mangyadanki a kan wuta kisanya albasa idan ya soyu seki zuba cincin dinki dakika yanka acikin man kina soyawa harsekinga yayi kalan burawun seki kwashe shikenan kin gama cincin yar uwa.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes




sharhai