Lemun cucumber da lemu

mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
Kaduna State, Nigeria

Lemun nan na da dadi sosai da amfani a jiki gashi natural.

Lemun cucumber da lemu

Masu dafa abinci 7 suna shirin yin wannan

Lemun nan na da dadi sosai da amfani a jiki gashi natural.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 2Cucumber guda
  2. 4Lemu mai bawo guda
  3. 4Lemun tsami guda
  4. 1Sikari kofi
  5. Ganyen na'a na'a kadan
  6. Ruwa dai dai bukata

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko ki wanke kayan hadin ki,sannan ki yanka cucumber ki zuba a blender sai ki zuba ruwa ki markada.Bayan kin markada sai ki tace ki aje a gefe.sai ki matse lemun ki tare da lemun tsamin shima ki tace ki aje gefe.

  2. 2

    Kiyi suga syrup,ki zuba sikarin a tukunya sai ki zuba ruwa kofi daya dai dai adadin sikarin sai ki jefa ganyen na,a na,an ciki ki daura a wuta ki barshi ya tafaso sikarin ya narke sai ki sauke ki barshi ya huce sai ki tace.sai ki zuba ruwan lemun da sugar syrup din cikin ruwan cucumber ki kara ruwa kadan ki juya ki sa a fridge yayi sanyi.A sha lafiya.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
rannar
Kaduna State, Nigeria

sharhai

Similar Recipes